Saturday, November 21, 2026
spot_img
Home News 2027: Timi Frank ya gargadi shugabannin Arewa da Kudu kada su fada...

2027: Timi Frank ya gargadi shugabannin Arewa da Kudu kada su fada tarkon Tinubu

Tsohon Mataimakin Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Kwamared Timi Frank, a ranar Laraba ya gargadi ’yan Najeriya kada su bari su fada cikin dabarun Shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake “kwace mulki” a shekarar 2027.

Frank, wanda ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar daga Abuja a ranar Laraba, ya bukaci shugabannin Arewa da na Kudu da kuma jam’iyyun adawa da su yi adawa da kokarin Tinubu na sake tsayawa neman shugabancin kasa a 2027.

Ya bayyana cewa, yayin da Tinubu ke amfani da barazana wajen neman goyon bayan ’yan Kudu musamman gwamnoni na jam’iyyun adawa irin su PDP, LP da APGA tare da amfani da kabilanci da bangaranci, a daya bangaren kuma yana barazanar kaddamar da dokar ta baci a jihohinsu da zargin tashin hankali da rashawa idan suka ki mara masa baya.

“Yanzu ya kara matsin lamba ta hanyar yi wa akalla gwamnoni biyar na PDP daga Kudu barazana da matsin lamba don su koma APC tare da ‘yan majalisunsu.

“A wurin Tinubu, zaben 2027 ya zama tsakanin shi da Arewa, shi ya sa yake ta kokarin jan hankalin Kudu ta hanyar dabara da yaudara. Ya manta da sauri cewa Arewa ce ta taimaka masa ya hau mulki a 2023,” in ji shi.

A cewar wannan dan rajin siyasa daga jihar Bayelsa, bai kamata zaben 2027 ya zama batun kudu ko arewa ba, ya kamata ya kasance kan wanda zai iya magance matsalolin da ke addabar kasa kamar kashe-kashe, garkuwa da mutane, da ta’addanci, da kuma halin kuncin tattalin arziki da cire tallafin man fetur, karin kudin wutar lantarki da tsadar kayan masarufi da sabis, wadanda shugaba Tinubu ya jefa talakawa cikinsu.

Ya ce: “’Yan Najeriya na bukatar shugaban da zai inganta kasar, ba wai ‘dan Arewa’ ko ‘dan Kudu’ ba ko ‘shugaban Arewa’ ko ‘shugaban Kudu’.

“Kasarmu ta riga ta cika da rarrabuwar kawuna bisa kabilanci. Bai kamata mu samu wani shugaban da ke haddasa gaba tsakanin yankuna domin cimma burinsa na kansa ba.

“Ni Timi Frank, a matsayina na dan Kudu, ban yarda da shugaba mai son raba kasa bisa kabilanci ba. Ina bukatar shugaba wanda zai hada Najeriya, ba wanda zai kara raba ta ba.

“Ina shawartar ’yan Arewa da suke goyon bayan Tinubu da su sake tunani. Ya kamata su gane cewa Arewar da ta taimaka masa samun mulki a 2023 ita ce ke shan wahala fiye da kowa a yau.

“Tabbas Arewa na fuskantar babbar gibin wakilci a gwamnati da shirye-shiryen raya kasa saboda fifikon da Tinubu ke baiwa bukatunsa na kai da na kabilarsa sama da komai.

“Dalilin da ya sa Arewa ya kamata ta farka. Su gane cewa hanyar da Tinubu ke bi wajen siyasar 2027 ba zai amfanar da Najeriya ba. Su tashi su hada kai da murya daya a 2027.

“Ina son shugabannin Arewa su gane cewa idan Tinubu ya samu damar sake hawa mulki a 2027, Arewa za ta ci gaba da fuskantar wariya da rashin kulawa domin Tinubu da APC ba su da wata sahihiyar damuwa da Arewa.

“A halin yanzu, akwai akalla gwamnoni biyar daga jam’iyyun adawa da ake shirin janyo su zuwa APC ba don suna kaunar Tinubu ba, sai don matsin lamba da barazana, yayin da wadanda za su zauna a jam’iyyunsu an tilasta musu su rattaba hannu a yarjejeniyar cewa sai sun kawo nasara ga Tinubu ko kuma a hana su dawowa kan mulki.

“Tinubu bai yi amanna da karfin zaben mutane ba. Yana kokarin sace sakamakon zabe kamar yadda ya yi a 2023.

“Idan Arewa ba ta gane hatsarin da ke gabanta ba, za ta yi nadama idan ba ta dakatar da Tinubu a 2027 ba.

“Tinubu bai yarda da dimokuradiyya ba, shi ya sa ya tabbatar da cewa PDP, LP da sauran jam’iyyun adawa sun fada cikin rikice-rikicen cikin gida domin hana yan takarar da suka cancanta damar kalubalantarsa a 2027.

“Burinsa guda daya shi ne ya ci gaba da rike mulki a 2027 ta ko wane hali, ko da hakan na cutar da ’yan Najeriya ne, wanda hakan ya matukar sabawa rantsuwar ofishin da ya dauka lokacin karbar mulki.”

Ya koka da cewa a halin yanzu Najeriya na tafiya kamar jirgi ba matuki a karkashin jagorancinsa, amma duk da haka yana son sake tilasta kansa kan ’yan Najeriya a 2027.

Ya kara da cewa: “’Yan Najeriya dole su shirya su ki amincewa da shi. Wannan shi ne abu mafi kishin kasa da za su iya yi. A matsayinsu na ’yan kasa, dole ne su ki shugaban da bai da hangen nesa kuma mara shugabanci, kuma su dauki duk matakan da suka dace na doka domin hana shi dawowa kan mulki.”

Ya kuma bukaci shugabannin adawa a kasar da su tabbatar da nasarar hadakar da suke yi domin kayar da Tinubu a 2027.

“Hadakar da ake yi a halin yanzu tana da amfani ga Najeriya da ’yan Najeriya. Don haka ina rokon shugabannin hadakar da su fifita Najeriya da al’ummar ta a gaba saboda shawarar da za su yanke za ta taimaka wajen sake gina kasar da makomarta,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here